MUHIMMAN ABUBUWAN DA KE BA DA DAMAR SHIGA1

  • Shekaru 16 zuwa sama, wanda tarihi ya nuna sun taɓa yin ciwon sikila (HbSS, HbSC, HbS/β0 thalassemia, Hb/β+ thalassemia, ko kuma wasu nau’ukan ciwon sikila)
  • A ƙalla tashin ciwon sikila sau 2 ko kuma yawan da bai haura sau 10 ba a cikin watanni 12 da suka wuce kafin a nema izini kafin samun amincewar mai jinyai
    • Wanda ke cikin rukunin tsananin ciwo, matsanancin ciwon ƙirji, matsalan tashin gaba, ko motsawan hanta ko saifa
  • Idan ana kan shan hydroxyurea, tsarin shan hydroxyurea ɗin dole ya zama ba fashi na tsawon a ƙalla kwanaki 90 kafin a fara binciken laluɓe cikin duhu

MUHIMMAN ABUBUWAN DA KE HANA SHIGA 1

  • Juna biyu ko shayarwa
  • Wanda ake wa ƙarin jini a-kai-a-kai
  • Mai ciwon hanta, tsananin ciwon hanta, ciwon maɗaci ko ciwon ƙoda mai tsanani
  • Wanda aka taɓa yi wa aikin ƙwayan halitta ko wanda aka taɓa yi wa dashen ɓargo ko ƙashi
  • Wanda yake kan shan voxelotor, crizanlizumab ko L-glutamine
  • Wanda yake kan karɓan kulawa ta jinyan ciwon hanta
  • Shan magani mai rage CYP3A4/5 ko mai saka CYP3A4