BAYANAN HAƘƘIN MALLAKA
SANARWAR HAƘƘIN MALLAKA DA IZINI MAI IYAKA
Duk abinda kuka gani kuma kuka ji a wannan kafar intanet ("ƙunshiya"), wanda ya haɗa da, misali, dukkan rubutu, gurin ajiya, hotuna, misalai, zane-zane, taƙaitaccen sautin murya, taƙaitaccen bidiyo, da taƙaitattun bidiyoyi na ji da gani, suna da haƙƙin mallaka a ƙarƙashin hukumar kula da haƙƙin mallaka ta ƙasa da ƙasa ta Amurka. Haƙƙin mallakan Ƙunshiyar mallakin Agios ne ko wasu masu alaƙa waɗanda suka ba wa Agios izinin amfani da kayayyakinsu. Gaba ɗaya abubuwan cikin shafin intanet ɗin nan suna da haƙƙin mallaka a matsayin aikin gamayya ƙarƙashin hukumar kula da haƙƙin mallaka ta ƙasa da ƙasa a Amurka. Agios ke da haƙƙin mallaka a wajen zaɓe, gudanarwa, shirye-shirye, da kuma tsarawa tare da inganta Ƙunshiyar. Za ku iya saukewa, ajiyewa, gurzawa ko kuma kwafar wani zaɓaɓɓen sashi na Ƙunshiyar wannan kafar intanet, matuƙar kun:
- Kun yi amfani kaɗai da abubuwan da kuka sauke domin amfanin kanku, amfanin da ba na siyarwa ba ko kuma don ku bunƙasa alaƙar kasuwancinku da Agios
- Kada ku wallafa ko yaɗa wani daga cikin abubuwan a kan duk wata kafar intanet ba tare da neman izini kafin yin hakan ba a rubuce daga Agios
- Kada ku sauya ko ku yi kwaskwarima ga Ƙunshiyar ta kowace hanya ko ku goge ko gyara wani haƙƙin mallaka ko alamar kasuwanci ko sanarwar sirri
Babu wani haƙƙi, laƙabi ko ra'ayi a Ƙunshiyar da aka sauke da aka ba ku yayin da kuka sauke Ƙunshiyar daga wannan kafar intanet. Agios na da dukkan haƙƙin kariyar fasaha a kan duk wata Ƙunshiya da kuka sauke daga wannan shafin. Sai dai kamar yadda aka bayyana ƙarara a sama, ba za ku kafa, sauke, gurza, wallafa, nuna, rarraba, sadar, sauya, fassara, gyara, haɗa, sabunta, tattara, rage ko bin kowace irin hanya ba domin sauyawa ko a mallakar dukkan ko wani ɓangare na Ƙunshiyar da aka sauke ba tare da kun nemi izini a rubuce ba daga Agios.
Idan kuna tunanin wani abu a cikin wannan shafin ya karya dokar haƙƙin mallaka, alama, sunan kamfani ko wasu haƙƙoƙin na daban, to ku ɗan turo da saƙon imel zuwa ga wakilin da aka naɗa na Agios a info@Agios.com.
SANARWAR ALAMAR KAMFANI
Dukkanin alamomin kamfani, shaidar aiki da tambarin kamfani da aka bayyana a shafin intanet ɗin nan ("Alamar Kamfanin(kamfanonin)") a alamomin kamfani nemasu rijista da marasa rijista na Agios ko wasu masu alaƙa da suka bada izini ga Agios. Kamar yadda aka bayyana a wannan ƙa'idoji da dokokin, ba za ku iya sake buga wa, nuna ko kuma yin amfanin da wani alamar kamfani ba tare da neman izini a rubuce ba daga Agios.
RA’AYOYIN DA BA A NEMA BA
Agios na maraba da sharhinku da martani game da wannan kafar intanet. Duk wasu bayanai da kayayyaki, da suka haɗa da sharhi, ra’ayoyi, tambayoyi, zane-zane da makamantansu, waɗanda aka bayar ta hanyar shafin za a ɗauke su ne a matsayin WAƊANDA BA NA SIRRI BA kuma BA NA MALLAKA BA. Saboda wannan dalili, muna buƙatar da kada ku tura mana wani bayani ko wani abu da ba za ku iya mallaka mana ba, abin da ya haɗa da bayanan sirri ko wani abun ƙirƙira na asali kamar kayayyakin ƙirƙira, lambobin sirrin kwamfuta ko zane-zane na asali. Idan kuka tura bayanai ko abubuwa ga Agios ta wannan kafar intanet, to ya nuna cewa kun mallaka wa Agios kyauta, duk wani haƙƙi na faɗin duniya, suna da ra'ayi a dukkan haƙƙin mallaka da kare haƙƙin fasaha a bayanai da abubuwan da kuka bayar. Agios sun samu damar amfani da duk wasu bayanai da abubuwan da kuka bayar ta wannan kafar intanet don yin amfani da shi kowane iri ne ƙarƙashin tsarin manufanmu, ba tare da wani hani ba kuma ba tare da an biya ku ba ta kowa ce hanya.
DOKAR SIRRANTAWA TA KAFAR INTANET
Danna nan domin ganin dokar sirrantawaR kafar intanet ta Agios wanda ya shafi amfani da bayananku da aka tara ta wannan kafar, waɗanda aka haɗa su da manazarta a matsayin ɓangaren ƙa'idoji da dokoki.
MAHAƊA ZUWA WASU SHAFUKAN
Shafin zai iya ƙunsan babban mahaɗi zuwa wasu shafuka waɗanda ba Agios ba ne ke sarrafa su. Ana samar da waɗannan manyan mahaɗan domin samun sauƙi da kuma manazarta kaɗai, kuma hakan bai nuna yarda a kan wasu kaya ko ayyuka waɗanda aka samar na wani wanda ke da alaƙa da waɗannan kafafen intanet, sannan ba ya nuna wata alaƙa da ake da ita da masu rarrafa su. Agios ba ta da iko a kan waɗannan kafafen intanet kuma ba ta da haƙƙi a kan abubuwa da suka ɗora. Agios ta barranta daga duk wasu abubuwa da wasu masu alaƙa ta daban suka saka a shafukansu waɗanda suke da mahaɗi zuwa shafinmu na intanet ko wasu kayayyaki ko ayyuka na wasu mutane na daban. Waɗannan kafafen intanet na wasu masu mutane na daban (da kuma kafafen intanet ɗin da aka haɗa da su) za a iya samun bayanai waɗanda suke ba daidai ba a cikinsu, tauyayyu, ko tsofaffi. Agios ba ta yi wakilci ba game da abubuwa ko ingancin kayan da suke cikin kafafen intanet ɗin da ba na Agios ba ko wasu kayayyaki ko ayyuka na wani mai alaƙa ta daban da ke cikin waɗannan kafafen intanet. Za ku shiga ne sannan ku yi amfani da waɗannan kafafen intanet (da kuma kafafen intanet ɗin da aka haɗa da su) bisa ra’ayin kanku.
HAKAN BA ZAI MAYE GURBIN SHAWARAN LIKITA BA
Bayanan da aka bayar a wannan shafin ba a kawo su da niyyar su maye gurbin shawarar ƙwararren likita ba game da kiwon lafiya ba. A kullun ku nemi shawarar likitanku ko ƙwararrun masu kula da lafiya game da duk wata matsalar lafiya ko jinya. Babu wani abu a wannan shafin da aka yi shi da niyyar gwajin asibiti ko yin magani.
BARRANTAR SAMUN TABBACI
Wannan shafin an samar da shi ne a halin "YANDA YAKE" "YANDA AKA SAMU" ba tare da ko wane irin garanti ba. Zuwa ga matuƙar bin dokokin da ke da akwai, Agios ta barranta ga dukkan samun tabbaci, faɗe, nufi ko tsayayye, ya haɗa da amma ba bai taƙaita ba ga, tabbaci na kasuwanci, cancanta a kan wata manufa, da kuma rashin saɓa hakkin wasu daban da garanti da ake nufi wanda ya taso a yayin alaƙa ko a yayin aiki. Ba tare da taƙaita bayanan da ke sama ba, Agios ba ta yi wakilci ba ko ba da tabbacin cewa wannan kafar intanet zai kasance a kowani lokaci ko waje ba, ko kuma sarrafa shi zai zama babu yankewa ko kuma kuskure ba. Agios ba ta yi wakilci ba ko ba da tabbacin cewar abubuwan da ke cikin shafin ba sa ɗauke da ƙwayoyin cutar baros, tsutsotsi ko waɗansu lambobi, waɗanda za su iya fitowa ta sigar ɓaci ko ɓarna ba. Idan amfaninku da kayayyakin ko shafin intanet ya haifar da buƙatar yin gyara ko saiya wani ɓangare, Agios ba ta da alhakin biyan kuɗin waɗannan matsalolin. Masu amfani suke da hakkin kare kansu ta hanyar saukewa, sabuntawa da kuma amfani da anti baros. Bayanai da aka wallafa a wannan shafin za su iya zama ba cikakku ba ko kuma su kasance tsofaffi, kuma za su iya kasancewa suna ƙunshe da kuskure ko kuskuren rubutu. Agios ba ta ba da tabbaci ko wakilci a kan, iya wa’adin daɗewa, inganci, dogoro, ko cikar ko sakamakon amfani da wannan shafin ba ko saɓanin hakan wanda ya taso daga wannan kafar intanet ɗin ko wani bayani ko kayayyaki, sabis, manhaja, rubutu, zane-zane da mahaɗi wanda aka shiga ko suke wannan kafar intanet ɗin. Saboda wasu dokokin ba su ba da damar cire wasu ƙa’idojin tabbaci ba, za ta iya yiwuwa waɗannan da aka cire ba su da tasiri akanku. Agios ba ta yi ikirarin cewa kayayyakin sun dace ba ko kuma za a iya sauke su a wajen Amurka. Samun shiga zuwa ga kayayyakin zai iya zama ya saɓa doka a wajen wasu mutane ko wasu ƙasashe. Idan kuka shiga kafar intanet ɗin daga wajen Amurka, kun yi hakan ne a karan kanku, kuma alhakin kiyaye dokokin yankinku ya rataya ne ga wuyanku.
IYAKAR NAUYI
Ku ne ke da haƙƙin kula da duk waɗansu ƙalubale da suka danganci amfani da wannan kafar intanet. Babu wani yanayi, da zai sa Agios ko wani daraktanta, jami’anta, ma'aikatanta, ko abokan hulɗarta su ɗauki alhaki kai tsaye ko saɓanin haka, na wata hasara ko ɓarna da ta taso daga amfani da ko rashin amfani da kafar intanet ko makamancin haka ko dogaronku da wani bayani a cikin wannan kafar intanet, ko da an ba wa Agios shawarar yiwuwar aukuwar wannan hasarar ko ɓarnar. Wannan cikakken iyaka ce ta nauyi da ta shafi duk wata hasara ko ɓarna ko ma wace iri ce, ko kai tsaye ko saɓanin haka, gama gari, na musamman, na hatsari, na sakamako, na misali ko saɓanin haka, wannan ya haɗa da, sannan bai taƙaita ba ga, salwantar bayanai, kuɗin shiga ko riba. Wannan iyakar tana da tasiri ko da matsalar da ake ikirari a kan kwantiragi aka yi, rashin kula, juye, tsauri, ko ma a kan ko wace irin matsala, kuma ko da an shawarci ɗaya daga cikin mahukunta Agios ko ana tunanin ya kamata ya san yiwuwar aukuwar ɓarnan. Idan wani ɓangare na wannan iyakar ya zama maras inganci ko wanda ba za a iya tilastawa a kan wani ba saboda wani dalili, to gaba ɗayan nauyin da ya rataya kan Agios game irin wannan yanayi wanda da an yi masa iyaka kafin nan ba zai wuce dala ɗari ($100.00) ba.
BARRANTA DAGA BIYAN HASARA
Kun yarda za ku tsare, biyan hasara, rashin cutar da Agios, ko jami’anta, daraktanta, ma'aikatanta, abokan hulɗarta, game da duk wani ikirari, aiki ko buƙata, wanda ya haɗa da ba tare da iyaka ba, kuɗaɗen shiga da na Shari'a waɗanda suka auku yayin amfani da kayayyaki (har da manhaja) ko karya wata doka na wannan yarjejeniyar. Agios za ta ba da sanarwa a kan lokaci na duk wani irin wannan ikirarin, sammaci ko sauraron ƙara wanda aka sanar da ita kuma za ta taimaka muku, da kuɗinku, a wajen kare duk wani ikirari, sammaci ko sauraron ƙara.
HUKUNCIN GUDANARWA DA HURUMIN DOKA
Agios ce take gudanarwa da sarrafa wannan shafin daga ofishinta da ke Hukumar Massachusetts a cikin ƙasar Amurka. Duk wani ikirari mai alaƙa da waɗannan ƙa'idoji da dokoki da kuma amfani da wannan shafin zai bi shari'ar Hukumar ta Massachusetts, ba tare da yin la'akari da saɓanin bambance-bambancen dokokinsu. Yayin amfani da wannan shafin, ku ba da dama a shari'ance a kotun tarayya da jaha ta Massachusetts na duk wani abu da ya taso ko kuma ke da alaƙa da wannan shafin, waɗannan ƙa'idoji da dokokin ko kuma amfaninku da wannan kafar intanet ɗin. Kotun tarayya da ta jiha na Massachusetts tana da cikakken iko akan duk irin waɗannan ayyuka.
RABUWADA RASHIN AFUWA
Idan aka samu wani daga cikin waɗannan Ƙa'idoji da Dokoki ba shi da inganci ko kuma ba za a iya tilastawa a kan wasu ba ta hanyar duk wata kotu mai adalci, sauran ɓangarorin Ƙa'idoji da Dokokin za su cigaba da zama da ƙarfinsu da kuma ingancisu. Idan aka samu wani daga cikin waɗannan Ƙa'idoji da Dokokin ba shi da inganci ko kuma ba za a iya tilastawa a kan wasu ba, wani ɓangare ne kawai zai samu cikkaken iko ta yadda har za a fahimce shi a matsayin marar inganci ko wanda ba za a iya jaddadawa ba. Babu wata afuwa ta wannan yarjejeniyar da za ta ci gaba da zama hujjar yin afuwa na wannan ƙa'ida ko wata doka.
ƊAUKACIN YARJEJENIYA
Wannan Yarjejeniyar da kuma Manufar Sirri sun ƙunshi ɗaukacin yarjejeniya tsakanin ku da Agios game da shigarku da amfani da wannan kafar intanet da Ƙunshiyarta kuma ba za a iya mata kwaskwarima ba sai dai Agios kaɗai ke iya yi, kamar yadda aka kawo a nan ko kuma ta hanyar rubutacciyar takarda wanda duka ɓangaroran biyu suka sa wa hannu. Agios za ta iya ba da dama da ayyuka a ƙarƙashin wannan yarjejeniyar da manufar sirri wa wani daban a kowani lokaci ba tare da an sanar da kai ba ko an nemi izininka.