Labaran Masu Ƙoƙari kan Cutar Sikila
Kowanne Mai Ƙoƙari kan Cutar Na Da Labari
Cike na ke da fata mai kyau dangane da kasancewata a cikin mutanen da suke ƙoƙari kan cutar.
Q: Me hakan yake nufi gare ka/ki kasancewarka/ki Mai Fama Da Cutar Sikila?
A: Gare ni, a matsayina na mai fama da cutar sikila hakan na nufin ina da damar da zan ci galaba a kan ƙalubale da yawa da muke fuskanta daga wannan cutar.
Q: Me ya sa kuka shiga RISE UP?
A: A koda yaushe ina neman hanyoyin da zan taimaka na ga abubuwa sun tafi dai ga masu fama da cutar sikila na bayana. Sababbun magunguna da gwaje-gwajen binciken da suke da tasirin samar da sauƙi sun sanya ni cikin zumuɗi.
A matsayin mu na masu ƙoƙari cutar sikila, muna faɗa da cutar ne ga kanmu kuma don wasu ma.
Q: Me hakan yake nufi gare ka/ki kasancewarka/ki Mai Fama Da Cutar Sikila?
A: Ina alfahari cewa zan yi magana da yawun matasa masu tasowa masu cutar sikila. Na sha tabbatar wa da mutane da yawa kada su yi mamakin irin abin da zan iya yi.
Q: Me ya sa kuka shiga RISE UP?
A: Masu fama da cutar masu ƙarfafa wa junansu gwiwa ne. Idan muka mayar da hankali a kan nasarar da muka samu, ba za mu bar cutar ta sarrafa mu ba.
A matsayina na mai ƙoƙari kan cutar sikila, ina cike da kyakkyawan fata don haka ba zan rayu cikin tsoro ba.
Q: Me hakan yake nufi gare ka/ki kasancewarka/ki Mai Fama Da Cutar Sikila?
A: Kasancewa mai fama da cutar kawai yana buƙatar ka zama mai juriya. Ina ƙoƙari na ga nayi rayu cikin walwala kowacce rana, ko da cutar ta so ta munana mun. Kuma hakan shi ke ƙarfafa min gwiwa.
Q: Me ya sa kuka shiga RISE UP?
A: Yana da muhimmanci ka/ki kasance a irin wannan RISE UP binciken saboda an fi la’akari da mutane masu ɗauke da cutar da kuma fahimtar mahangarmu. Kasancewar yawan masu fama da cutar a cikin binciken, za a fi samun wasu damarmakin.
Ka/ki zama mai ƙoƙari kan cutar sikila na nufin kai/ke mai faɗa da cutar ne.
Q: Me hakan yake nufi gare ka/ki kasancewarka/ki Mai Fama Da Cutar Sikila?
A: Ina kallon ‘yan’uwana masu fama da cutar hakan na ƙara min himma. Mun mayar da hankali wajen duba wasu damarmaki da za su taimaka mana mu ci gaba. Idan akwai yiwuwar yadda ake rayuwa da cutar sikila a yau ya bambamta da yadda masu cutar na nan gaba za su kasance, ke nan hakan zai riƙa ƙarfafa mun gwiwa kodayaushe.
Q: Me ya sa kuka shiga RISE UP?
A: Yana da muhimmanci a gare mu mu halarci RISE UP binciken, ba wai kawai don kanmu ba, sai don duka masu fama da cutar. Za mu iya tabbatar da cewa masu cutar sikila na nan gaba za su fi samun dama a kan kiwon lafiyarsu.
Masu ƙoƙari kan cutar sikila na fuskantar cutar da ƙwarin gwiwa.
Q: Me hakan yake nufi gare ka/ki kasancewarka/ki Mai Fama Da Cutar Sikila?
A: Kasancewar ka/ki mai fama da cutar na nufin dagewa da yin aiki tuƙuru wajen magance ƙalubale. Ka yi/ki yi ƙokari kada ka/ki bar cutar ta dakatar da kai/ke, ko da a lokacin da kake/kike fuskantar tsanani ne.
Q: Me ya sa kuka shiga RISE UP?
A: Ina so na taimaka wa masu fama da cutar da wasu damammaki da za su sa su sami sauƙi rayuwa. Bincike irin na wannan RISE UP na da tasiri wajen sauya yadda za mu fuskanci cutar. Magana ake a kan a bar mu mu yi aiki kuma mu samo mu kawo wa iyalanmu, mu ɗauki lokaci da masoyanmu, kuma mu ji daɗin rayuwarmu
Ka yi/ki yi magana Ka/ki jajirce Yi magana da ƙarfi Ba da shawara Ba za a bar mu a baya ba.
Kasancewa a cikin RISE UP a matsayina na mai ƙoƙari kan cutar ya ba ni ƙwarin gwiwar da ban taɓa tunanin cewa ina da irinsa ba.
Q: Me hakan yake nufi gare ka/ki kasancewarka/ki Mai Fama Da Cutar Sikila?
A: Masu fama da cutar sikila mutane ne na musamman. Muna da ƙarfin hali saboda akwai buƙatar mu zama hakan. Ina samun ƙwarin gwiwa a kan gobe sanin cewa ina iyaka ƙoƙarina wajen taimaka wa kaina, da ma wasu masu cutar.
Q: Me ya sa kuka shiga RISE UP?
A: Yana da muhimmanci ka/ki zama jarumi/jaruma, ku yi magana a kan cutar sikila kuma a ɗauki kyakykyawan mataki.
YI SHIRI DOMIN WANI RUKUNIN BINCIKEN RISE UP NA GABA
Samu ƙarin bayani game da binciken RISE UP, ciki har da cikakken bayani game da yadda ake shiga, da dukkannin manufofin binciken, da muhamman abubuwan da ke ba da damar shiga da waɗanda ke hana shiga. Daga nan sai ku yi magana da majinyatanku da suka cancanci shiga dangane da binciken.
Idan kana da tambayoyi, tura saƙon imel ga:
medinfo@agios.com (Amurka)
ex-usmedinfo@agios.com (wajen Amurka)
An biya masu ƙoƙari kuma ba lallai su halarci binciken RISE UP ba.
An biya diyya ga masu ƙoƙari kan cutar sikila kuma ba lallai su iya kasancewa a cikin RISE UP ba. Mai ƙoƙari kan cutar sikila batu ne da aka ƙirƙire shi don mutane masu cutar su yi amfani da shi.
Ana nufin mutane masu ƙoƙari kan cutar sikila.
Ba a ba da damar amfani da Mitapivat a matsayin maganin sikila ba.
Mitapivat ba a amince da shi ba wajen magance cutar sikila.