Tambayoyin da aka + fi yi da abubuwan da ake amfani da su

Amsoshi ga masu ƙoƙari kan cutar sikilar

 / 
Mene ne zai faru da farko idan na yanke shawarar shiga cikin binciken?

Kafin ka shiga RISE UP a matsayin maihalarci, ‘yan tawagar binciken za su duba lafiyarka da tarihin lafiyarka don tabbatar da cewa za ka iya kasancewa a cikin binciken. Duba wajen yanke shawarar kasancewarka a cikin binciken don ka samu tabbacin ko wannan binciken ya dace da kai.

Waɗanne sakamako aka samu daga mataki na 2?

Mataki na 2 na RISE UP binciken na duniya ya nuna a lissafe yadda aka samu ƙarin tasirin furotin ɗin da ke ɗaukar iskar da ake shaƙa sama da sati 12 akan mitapivat yayin da aka kwatanta shi da placebo.

Adadin majinyata 79 aka yi wa rijista a mataki na 2 na RISE UP a duniya. A yayin da majiyanta 27 ne suka karɓi placebo, akwai kuma majinyata 52 da suka karɓi mitapivat.

Maganin Mitapivat ya ƙara rage tsitstsinkewar ƙwayoyin jini yayin da erythropoiesis ke ƙara yawan ƙwayoyin jini, idan aka kwatanta shi da placebo ba. Abubuwan da ake amfani da su wajen gwada lafiyar ƙwayoyin jini suna faɗa maka/ki ya lafiyar ƙwayoyin jininka/ki suke, su kuma erythropoiesis na faɗa maka/ki ya saurin yadda ake samar da ƙwayoyin jinin yake.

Maganin Mitapivat ya nuna yadda aka rage kaso 50% na ciwon da ake fuskanta (SCPC) fiye da yadda idan aka kwatanta da placebo.

Za ayi amfani da masu ba da kiwon lafiyar da suka yi a mataki na 2 da na 3 ne?

Eh, masu ba da kiwon lafiyar da suka yi a mataki na 2, su ne za a sake amfani da su a mataki na 3 har da ƙarin wasu ma.

Me ka sani dangane da mitapivat?

An jima ana bincike akan Mitapivat tun watan Maris 2014.

Majinyata sama da 700, da ya haɗa da ‘yan sa kai masu ƙosasshiyar lafiya aka warkar da maganin mitapivat a kan cututtuka daban-daban.

An jima ana bincike akan Mitapivat sama da shekara 5.

Takamaimai mene ne”magungunan da ke ingiza cuta” za suyi da ni? Shin hakan zai iya canja ƙwayar halittata ta DNA?

Maganin Mitapivat a matsayinsa na magani mai ingiza cuta zai samar maka da sauƙi ne ga cutarka, amma ba zai canja ƙwayar halittarka ta DNA ba.

Ina da tabbacin kasancewa a cikin masu shan maganin?

A zangon mataki na 3 na binciken, a duk cikin mutun uku na mahalarta binciken, biyu za su sha mitapivat ɗaya kuma zai sha placebo.

Kodayake, akwai halarta ta shekara 4 ta ganin dama na zangon gwajin bayyane inda kowa zai karɓi maganin mitapivat.

Shin mitapivat ba shi da haɗari?

Manufar wannan binciken na mataki na 3 shi ne don a gane cewa mitapivat yana aiki kuma ba shi da haɗari.

Ba majinyacin da ke shan mitapivat ko placebo da zai dena sha sabida illolinsu a zangon mataki na 2 na binciken.

A binciken maganin mitapivat, illolin da aka gani suka kai kaso 10% ga majinyaci sun haɗa da ciwon kai, jin gajiya, tashin zuciya, ciwon gaɓoɓi da kuma cutar COVID-19.

Zan iya shan wasu magungunan lokacin gwajin binciken?

Mitapivat zai iya canja tasirin aikin wasu magungunan, haka zalika sauran magungunan za su iya canja tasirin aikin Mitapivat ɗin shi ma. Shan mitapivat tare da wasu magungunan zai iya cutarwa.

Ka yi/ki yi magana da likitanka/ki akan cewa yanzu kana/kina shan wasu magungunan (da suka haɗa da magungunan da likitanka ya ba ka sharaɗin shan su, magungunan da ka gani ka siya bisa raɗin kanka da wasu ƙari, da ma kowanne nau’i da ya ƙunshi ɗan ice). Likitanka/ki zai sanar da kai/ke waɗanne magunguna ne suke ba su da haɗari don ka ci gaba a halin kana/kina shan mitapivat.

Tsawon yaushe na ke da buƙatar kasancewa a cikin binciken?

Idan ka shiga binciken, kasancewa a cikin mataki na 3 na binciken shekara ɗaya ne.

Kuna ɗiban sababbun majinyata ne don mataki na 3?

Eh, muna so ka kasance a cikin tafiyar. Yi rajista a nan.

Waɗanne asibitoci ne ke binciken mataki na 3?

Nijeriya

Me ake nufi da “gwajin maganin da ba ya aiki, da kuma gwajin ɓoye”?

Placebo magani ne da ya yi kama da maganin gaske amma ba ya magani. Placebos suna taimakawa ne wajen gwada tasirin sabon maganin da ake bincike a kai. “Gwajin ɓoye” na nufin kai/ke ko likitanka/ki ba wanda ya san cewa placebo za ka ɗauka ko maganin da ake bincike a kai don kada a sauya sakamakon bisa san zuciya.

Ta yaya za a iya kiyaye mun sirrina?

A lokacin aiwatar da binciken, sunanka/ki da ma dukkanin bayanan lafiyarka/ki za a adana su cikin sirri. Kowanne mahalarci na binciken za a ba shi lambar gane kai ta musamman. Abin da aka yi rekodin da bayanan da aka ɗauka lokacin binciken ba za su ƙunshi sunanka ba ko wani bayani da za a iya gane ka, sai dai kawai wannan lambar ta gane kai kawai.

Wanne irin taimako zan iya tsammani a lokacin binciken?

Kana/kina da abubuwa da yawa da suke faruwa a rayuwarka/ki, haka ma faɗa da cutar sikilar shi ma babban ƙalubale ne a kullun. Idan kana/kina buƙatar wani taimako lokacin binciken, za a iya samar da taimakon don:

  • Masu ba da kulawa
  • Rainon yaro
  • Tafiya
  • Sufuri
  • Albashi
  • Masu ba da jinya daga nesa
  • Ziyarta ta yanar gizo

Ayyukan da aka zayyana a sama na bisa doka da ƙa’idojin ƙasa ne. Yi haƙuri ka duba tare da mai bincike na gida don tabbatar da waɗanne ayyuka ne a yankinka/ki. Akwai bayanai dangane da agaji, yana nan a shafin yanar gizo da ka yi rijista.

Na ɗaya daga cikin babban abin da yake ƙarfafa mun gwiwa don ci gaba da faɗa da cutar shi ne mutanen da suke da cutar.

Teonna,

Mai Ƙoƙari kan Cutar Sikila

@sicklequeent