Dangane da Mitapivat
MAGANIN NAZARI ME TASIRI
Me yasa ake bincike dangane da Mitapivat yanzu
Maganin Mitapivat: shi ne maganin da ke da tasiri wajen ƙara ƙarfin jiki gami da rage ƙwayoyin jinin da ke da cutar sikilar Manufar RISE UP shi ne don a san tasirin maganin da kuma sanin rashin haɗarinsa wajen magance zugi da raɗaɗin ciwon da ke cikin ƙwayoyin jini. Idan hukumar FDA ta amince da maganin mitapivat to shi ne maganin da zai zama waraka ga cutar sikila.
Ƙwayoyin molikul na maganin na haɗuwa da wani sinadari da ke cikin jinin hakan sai ya haifar da samun ƙarfi. Wannan yana da tasiri wajen ƙara ƙarfi da kuma rage adadin jinin da ke ɗauke da ƙwayoyin sikilar.
Ga hujjoji
Akwai bayanai da yawa. ka saki jiki ka yi tambayoyi har sai ka samu nutsuwar shiga cikin binciken. Idan ka yanke shawarar ka shiga cikin binciken, kiyaye lafiyarka shi ne abin da za a fi bai wa muhimmanci. Ƙara sanin a shafin Tatsuniyoyi da na gaskiya.
Mai Ƙoƙari kan Cutar Sikila
Mai Ƙoƙari kan Cutar Sikila
YI SHIRI DOMIN WANI RUKUNIN BINCIKEN RISE UP NA GABA
Samu ƙarin bayani game da binciken RISE UP, ciki har da cikakken bayani game da yadda ake shiga, da dukkannin manufofin binciken, da muhamman abubuwan da ke ba da damar shiga da waɗanda ke hana shiga. Daga nan sai ku yi magana da majinyatanku da suka cancanci shiga dangane da binciken.
Idan kana da tambayoyi, tura saƙon imel ga:
medinfo@agios.com (Amurka)
ex-usmedinfo@agios.com (wajen Amurka)
An biya masu ƙoƙari kuma ba lallai su halarci binciken RISE UP ba.
An biya diyya ga masu ƙoƙari kan cutar sikila kuma ba lallai su iya kasancewa a cikin RISE UP ba. Mai ƙoƙari kan cutar sikila batu ne da aka ƙirƙire shi don mutane masu cutar su yi amfani da shi.
Ana nufin mutane masu ƙoƙari kan cutar sikila.
Ba a ba da damar amfani da Mitapivat a matsayin maganin sikila ba.
Mitapivat ba a amince da shi ba wajen magance cutar sikila.