Ƙa'idojin Amfani
ƘA'IDOJI DA DOKOKIN AMFANI DA KAFAR INTANET TA AGIOS
GABATARWA
Barka da zuwa shafin gwajin magani na shirin Agios na RISE UP ("kafar intanet”). Agios ta ƙirƙiri wannan kafar intanet da samar da bayanai da kuma sadarwa da likitoci cikin inganci, masu jinya, masu hannun jari da wasu waɗanda suke da ra'ayin ƙara sani game da abubuwa da ayyukan da Agios suke yi. Za ku iya amfani da wannan kafar intanet, matuƙar kuka bi waɗannan ƙa'idoji da dokokin. Ƙari kuma bisa waɗannan ƙa'idoji da dokoki, ya kamata ku karanta kuma ku san Dokokinmu na Sirrantawa, waɗanda suka bayyanar da amfanin Agios game da karɓa da sarrafa bayanan kanku, da kuma wasu manufofi da suke jagorantan shafinmu.
AMINCEWA DA WAƊANNAN ƘA'IDOJI DA DOKOKIN
Ku ɗauki ‘yan mintuna kaɗan don sake nazartar ƙa'idoji da dokokinmu. Idan kuka shiga wannan kafar intanet, to ya nuna cewa kun yarda za ku kiyaye kuma ku bi ƙa'idoji da dokokinmu. Idan ba ku yarda ku bi kuma ku kiyaye ƙa'idoji da dokokinmu ba, to ba sai kun shiga, ko kun yi amfani da shi ko kun sauke abubuwa daga kafar intanet ɗinmu ba.
WAƊANNAN ƘA'IDOJI DA DOKOKIN NA IYA SAUYAWA
Agios na da dama ta yi gyara ko ta sauya waɗannan ƙa'idoji da dokoki a ko wane lokaci ba tare da ta yi sanarwa ba. Amfaninku da wannan shafin na intanet bayan an yi wani sauyi ya nuna yardarku na bi da kuma kiyaye ƙa'idoji da dokokinmu kamar yadda aka sauya. Saboda wannan dalili, muna ba ku shawara da ku sake duba waɗannan ƙa'idoji da dokokin namu duk lokacin da kuka ziyarci shafin mu.
An sake bitar waɗannan ƙa'idoji da dokoki na ƙarshe a ranar 28 ga Yuni, 2018