Yanke shawarar shiga gwajin binciken cutar

Me ake da buƙata don kasancewarka a cikin RISE UP

Teonna, Sickle Cell Warrior
TEONNA,

Mai Ƙoƙari kan Cutar Sikila

Dalilan da ya sa RISE UP ya dace da kai/ke

Abubuwan da ake da buƙata domin samun cancanta:

  • Ka/kin kai shekara 16 ko fiye da haka
  • An gano cewa kana/kina da cutar sikila
  • Idan kai/ke ko matarka na iya yiwuwa ta ɗau juna biyu, dukkan ku ana da buƙatar kuyi amfani da hanyoyi biyu na kare kai daga ɗaukar juna biyu
  • Ka/kin fuskanci aƙalla tsananin ciwo sau 2 ko dai bai wuce sau 10 ba a shekarun baya
    • Hakan na nufin zafin ciwon da ake fuskanta na buƙatar agajin lafiya kuma sun samu ne sabida zafin ƙirji, miƙewar azzakari, ko kuma toshewar kafafen jini a hanta, saifa, ko kuma a wani gurin a cikin jiki
  • Matakin furotin ɗin da ke ɗaukar iskar da kake/kike shaƙa yana tsakanin 5.5 ko 10.5 g/dL
  • Idan kana shan hydroxyurea, ana da buƙatar ka ci gaba da shan wannan adadin na tsawon kwanaki 90 kafin ka fara shan wannan sabon maganin
DeMitrious, Sickle Cell Warrior
DeMITRIOUS,

Mai Ƙoƙari kan Cutar Sikila

Dalilan da ya sa RISE UP ba zai dace da kai/ke ba

  • Idan kina da juna biyu ko kina shayarwa
  • Idan ana maka/ki ƙarin jini a-kai-a-kai
  • Idan kana/kina da wata matsala da ta shafi hanta ko ciwo a matsarmama
  • Idan kana fama da matsanancin ciwo a koda
  • Idan ka/kin fuskanci dashe na ɓargo ko dashen ƙwayar halitta
  • Idan yanzu kana/kina shan wani magani na cutar sikila (kamar voxelotor, crizanlizumab, ko L-glutamine) amma ban da hydroxyurea
  • Idan yanzu kana/kina shan maganin da yake ƙara jini, kamar erythropoietin

Samun mahalarta binciken da yawa zai ƙara ba da fahimtar zaɓi da kuma damarmaki gare mu. Alheri ne ga kowa.

Golie,

Mai Ƙoƙari kan Cutar Sikila

@golielorenzo